Thursday, July 16
Shadow

Tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka fiye daga kasashen Amurka, Ingila, da Jamus>>Inji Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa, Tattalin arzikin Najeriya zai samu habaka sosai fiye dana kasashe masu arziki irin su Amurka, Ingila, da Jamus.

Me magana da yawun shugaban kasa, Daniel Bwala ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na X inda yake martani kan bayanan habakar tattalin arziki da kungiyar bayar da lamuni ta Duniya, IMF ta fitar.

IMF tace Najeriya zata samu habakar tattalin arziki da maki 4.1 a shekarar 2026.

Wannan maki yafi na kasar Amurka wanda IMF tace 2.3 ne sannan yafi na kasar Ingila wanda IMF tace 0.8 ne hakanan yafi na kasar Jamus wanda shima 0.8 ne.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Wasu matuka jirgin sama na Najeriya na shan Wiywiy, wani lokacin sai na hau jirgi idan na ga yanayin Direban sai in sauka saboda tsaro>>Inji Sanata Orji Uzor Kalu

Daniel yace Gwamnatin Tinubu ba da wasa take ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *