
Wata Kungiyar matasa magoya bayan Peter Obi sun bayyana cewa, a yanzu basa son Peter Obi, tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan suke son ya fito ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.
Matasan sun ce ya zamarwa Goodluck Jonathan dole ya amince da wannan bukata tasu.
A dasu ne dai wasu matasa suka je kofar gidan tsohon shugaban kasar inda suke kiran da ya fito takarar shugaban kasa amma yace zai yi shawara tukuna.