Gishiri na da tasiri sosai abubuwan rayuwar al’umma daban-daban, kama daga abinci, da kuma yanayin rayuwa na yau da kullun.
Ana amfani da Gishiri wajan hada sirrin Mallaka, Saidai a yayin da wasu wannan sirri na musu aiki, wasu baya musu aiki.
Amma abin tambaya anan shine, menene ingancin sirrin mallaka na gishiri?
Masu iya magana sun ce,tsafi gaskiyar maishi, ga wasu, wannan sirri zai yi amfani kamr yanda muka bayyana a sama, ga wasu kuma ba zai yi amfani ba, ya danganta ga karfin imanin mutum akan aikin wannan abu.
Babbar Hanyar Mallaka kamar yanda muka bayyana a baya shine ta hanyar kyautatawa a bangaren ma’amala, kyauta,da kuma kalamai masu dadi.