Alwala ta wadatar wajan tsarkin Maziyyi, ba sai an yi wanka ba.
Hakanan Maziyyi najasa ne, dan haka duk inda ya taba a jikin mutum sai an wankeshi.
Saidai idan ya taba tufafin mutum,kayan sawa, yayyafa ruwa a wajan kawai ya wadatar.
An tambayi Annabi Muhammad (Sallallahu Alaihi wasallam) game da tsarkin Maziyyi akan kayan sawa,sai yace a cika hannu da ruwa a yayyafa a wajan da ya taba kayan ya wadatar. At-Tirmidhi (115)
Allah ne mafi sani.
Maganin samun hipsMaganin samun hips