
Wadanda suka je kallon wasannin kofin Duniya a kasar Amurka sun bayyana cewa, Amurkawa sun cika rokon kudi.
Sun bayyana cewa ko ruwa mutum ya siyasa a shago sai kaji mutum yace wai a bashi kudi.
A kasar Amurka, al’adar rokon Kwastoma kudi kyauta idan yayi siyayya ba sabuwar abu bace, da yawa zaka ga albashin da ake biyan ma’aikata babu yawa amma ta wajan kyautukan da ake basu anan suke samun kudade masu yawa da zasu iya rike kansu.
Wasu sun yi bayanin cewa, su sunfi gane a gaya musu ainahin farashin kaya su saya maimakon a basu kaya da sauki amma kuma a rika rokonsu kudi.