Thursday, July 2
Shadow

Wata Sabuwa: An gano tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayar da takardun karya dake nuna cewa bashi da lafiya dan a bayar da belinsa

Rahotanni sun bayyana cewa, An gano tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya gabatarwa da babbar kotu a jihar Kaduna takardar da yace babban Asibitin kasa ne ya bashi data tabbatar da cewa bashi da lafiya dan a bayar da belinsa.

Saidai ICPC dake karan Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ta bayyana cewa Daraktan Asibitin na kasa, Professor Muhammad Raji Mahmud, ya karyata cewa asibitin bai baiwa malam Nasiru Ahmad El-Rufai takardar cewa bashi da lafiya ba.

ICPC ta gabatar da takardar da babban asibitin na kasa ya bayar wadda ta tabbatar da cewa Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bai ma taba zuwa Asibitin dan a duba lafiyarsa ba.

Karanta Wannan  Hoto: Davido ya nuna yanda yayi zabe a kasar Amurka, Saidai 'yan kasar Africa ta kudu sunce karya yake a bola ya dauki kuri'ar yayi hoto da ita dan ace shi dan America ne

Da wannan ne kotun tace ba zata bayar da belinsa ba akan cewa wai bashi da lafiya.

Saidai kotun tace ICPC kada ta hana Likitansa ya rika dubashi sannan idan yana son zuwa kowane asibiti ne a fadin Najeriya kada a hanashi, a rakashi da jami’an tsaro.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *