Ruwan infection dake fitowa daga gaban mata yana da kaloli da yawa.
Wanda ba na infection ba, fari ne me yauki.
Amman ruwan infection, yakan iya zama da kalar Green ko a ce ruwan kore ko kalar ganye.
Fitowar ruwa kalar ganye,ko ace green ko ace kore, yana iya zama alamar cutar sanyi wadda akan dauka lokacin jima’i ko a bandaki mara tsafta.
Hakanan irin wannan ruwa kan iya zama matsalar cutar yoyon fitsari.
Sai kalar Grey/Gray ko ace kalar ruwan toka ba me duhu ba.
Idan kika ga ruwa me kalar Grey/Gray ko kalar ruwan toka ba me duhu ba a gabanki to alamar cutace, musamman idan ya zamana kina jin zafi lokacin da kike fitsari.
Yawanci antibiotic suna maganin irin wannan matsalan, amma idan ya tsananta a tuntubi likita.
Ruwa me kalar ja ko kalar Yellow, ruwan dorawa, ko Brown, me ruwan kasa, ko pink, me kalar tsatsa, idan ya fito daga gabanki, yawanci ba alamar matsala bane.