Jarumar fina-finan Kannywood, Amal Umar ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu mutane na yaɗa mummunar fahimtarsu game da halayen wasu jaruman shirya fina-finan.
Amal Umar -wadda ta bayyana hakan cikin shirin Mahangar Zamani na BBCHausa – ta ce babban takaicinta shi ne yadda ake yi wa ƴan fim kallon marasa tarbiyya.
Duk da cewa akwai labarai marasa daɗi da ake yaɗawa game da masu sana’ar fim, jarumar ta nesanta kanta daga dukkan zarge-zargen da al’umma ke yi wa ‘yan fim.
‘’Kowa ba ya yi mana zaton alkahiri, sai dai ki ji ana karuwai ne su, ba su kwana a gidajensu, sun raina iyayensu, irin waɗannan abubuwan, amma ni na sani, kuma masu mu’amula da ni sun sani, duk daren duniya idan na gama abin da nake yi sai na kwana a gidanmu’’, in ji jarumar.
Sauran baƙin da shirin ya tattauna da su, Abubakar Bashir Maishadda da Abdulaziz Ɗan Small sun ce akwai mutanen da suke ɗaukar wa kansu cewa dole sai sun bibiyi ƴan fim da sharri, saboda haka ne suke yaɗa labaran ɓatanci a kan jarumai, da kuma masana’antar.
‘’Kin san abin da na gano? Akwai wanda duk duniya idan bai taɓa ƴan fim ba gani yake babu wanda zai san shi”.
”Musamman yanzu da kawai sai mutum ya buɗe shafin Youtube ko TikTok ya ce bari in ja mabiya (Followers), ya yaɗa sharri sai bayan kwana biyu ido ya raina fata’’ in ji Abdulaziz Ɗan Small.
Jaruman sun kuma musanta jita-jitar da ake yaɗawa cewa ana ɓata tarbiyar sabbin jarumai kafin shigar da su harkar fim.
‘’Da abin da kika zo, da abin da za a bi ki da shi ke nan’’ in ji jaruma Amal Umar.
Dukkan jaruman sun kore mummunar fahimtar da ake yi masu, kodayake sun yarda cewa akwai wasu lokutan da ake samun wasu can daban masu aikata laifin da ake yi wa jaruman kuɗin goro da su.
A cewar jaruman akwai mutane da ke ɓata wa Kanywood suna a idon duniya, waɗanda su ba ma ‘yan fim ba ne.
A nasa ɓangaren, Bashir Maishadda ya ce lokaci ya yi da za a samu fahimtar juna tsakanin ƴan fim da masu kallo, da ma sauran jama’ar gari, ta yadda ”duk lokacin da aka ga wani kuskure ko abin gyara a cikin harkar za a iya bayar da shawara domin samun mafita.
Jaruman Kannywood dai sun sha fitowa suna bayyana takaici game da yadda ake samun masu ɓata masu suna a cikin al’umma, lamarin da suka ce yana zubar da mutuncinsu a idon duniya.