A sassa daban-daban na Duniya an Amfani da zuma wajan maganin ciwon ido.
Ta tabbata cewa, amfani da zuma me kyau wadda bata da hadi na maganin ciwon ido da kumburin idon da kuma ma kaikayin idon.
Zuma tana maganin ciwon ido daban-daban.
Misali ana hadata da ruwan gishiri a rika digawa a ido me ciwo.
Zuma na da matukar amfani sosai wajan magance matsalar bushewar ido inda ake hada ruwa da zuma a rika digawa a idon.
Tana maganin tattarewar fatar ido. Mafi yawan magungunan hana tsufan fata suna da illa idan aka shafasu a kusa da ido.
Saidai ita Zuma bata da wata illa idan aka shafata a kusa da ido, ana hadata da ruwan gishiri, man kwakwa, ko kuma zallan ruwa a rika shafawa a gefen ido, tana hana tattarewar ido da sawa fatar jikin ido ta yi tas da haske.
Yanda ake amfani da zuma wajan maganin ciwon ido:
Kada a sake a diga zuma kai tsaye a cikin ido ko a shafata kai tsaye a gefen ido ba tare da hadata da ruwa ba.
Ana iya samun ruwa kofi 1 a zuba zuma karamin cokali 5 a tafasa a barshi ya huce a rika wanke ido dashi ko kuma a rika digawa a cikin idon. Ana kuma iya hadawa da ruwan gishiri.
Ana kuma iya ajiye sauran ruwan a firjin dan amfani dashi nan gaba.
Yana da kyau a tuntubi likita dan neman karin shawara.