Sunday, August 30
Shadow

Shugaba Tinubu ya baiwa Kotun Amurka hujjoji 4 da yace ta yi La’akari dasu kada ta fitar da bayanan dake kunshe da zargin safara Qaya da ake masa

Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya baiwa kotun kasar Amurka Hujjoji 4 da yace ta yi la’akari dasu kada ta fitar da bayanan sirri dake kunshe da zargin da ake masa na safarar qaya.

Shugaban ya bayyana hakane ta hannun Lauyoyinsa Christopher Carmichael, Victor Henderson da Oluwole Afolabi.

Ya bayyana cewa babu dalilin da zai sa sai mutane sun san bayanan dake kunshe a cikin zargin da ake masa.

Sanan yace ana son a yi amfani da bayanan ne wajan cimma wani buri na siyasa.

Shugaban ya kuma ce dokar Amurka ta bashi kariya kan wannan bayanai tunda abune wanda ya shafeshi shi kadai dan haka sirrinsa ne.

Karanta Wannan  Mutane 2 sun mutu wasu da dama sun jikkata bayan fashewar bam a jihar Imo

Jam’iyyun Adawa da kungiyoyin fafutuka da yawa sun nemi a bayyana wadannan bayanai inda suke cewa ‘yan Najeriya na da damar sanin irin rayuwar da shugaban kasar yayi a baya.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *