
Taron malam Arewa 500 a Jihar Jigawa inda suka ce a sabi Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a 2027 ya jawo cece-kuce.
Wasu daga cikin malaman da suka halarci wajan sun fito sun barranta kansu da kalaman cewa wai a zabi Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a 2027 inda suka ce basu amince da hakan ba.
Wasu kuma suka yi zargin cewa yaudararsu aka yi zuwa wajan Taron.
Saidai a yanzu a samu wani Malami ya fito ya bayyana cewa kowane Malami an bashi Naira Miliyan 3 ne a wajan Taron.