Monday, August 31
Shadow

Kalli Bidiyon: Matashi dan Arewa Saleem Top da ya shahara wajan karatun Qur’ani a kafafen sada zumunta ya jawo cece-kuce bayan da aka ga ya koma Waka

Matashi dan Arewa, Saleem Top da ya shahara wajan Karatun Qur’ani a Tiktok yana da mabiya Miliyan 8 ya jawo cece-kuce bayan da ya koma waka.

Daga cikin masu bibiyarsa hadda shahararren dan kwallon kafa, Usman Dembele.

An ganshi da Jita yana wakar yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)saidai hakan ya jawo cece-kuce saboda yanda aka ga Bidiyon wakar da yake baya daukar hankali kamar Bidiyon karatun Qur’ani da ya saba yi.

Hakanan an fara rade-radin cewa, Dembele din ma da yake bibiyarsa ya daina.

Dan hakane wasu suke bashi shawarar ya daina wakar.

@danjibur_kk

GASKIYA WANNAN LAMARI YA TADA KURA, AMMAN DAI KOWA DA IRIN FAHIMTARSA✍🏽💯👌🏽 #dembele #saleemtop #alquran #music #arewa

♬ original sound – 𝐃𝐀𝐍𝐉𝐈𝐁𝐔𝐑_𝐊𝐊🏟
Karanta Wannan  Gyaran filayen jirgin sama: Hadimin Ganduje Salihu Tanko-Yakasai ya soki Tinubu, ya ce “Emi Lokan” ta zama “Lagos Lokan”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *