Saturday, September 5
Shadow

Yanda aka kori daya daga cikin masu gadin hukumar ICPC saboda ya shigar da matar tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai wajan da ake tsare dashi ta ganshi a Asirce

Rahotanni sun bayyana cewa Hukumar ICPC ta kori daya daga cikin masu gadinta me suna Daniel Stephen bayan da ya shigar da matar tsohon gwamnan Kaduna, Aichatou Asabe El-Rufai wajan da ake tsare dashi a asirce suka gana.

Rahotanni yace an ga Daniel a kyamarar CCTV yana budewa Asabe kofar baya ta ma’aikatar inda ta shiga wajan mijinnnata suka yi magana da hausa ta tsawon mintuna 15.

Daniel dai da kansa ya rubuta takardar cewa ya amince da aikata laifin da ya sabawa ka’idar aiki kuma daga nan ne aka koreshi daga aiki.

Mahukunta sunce ba yaune Daniel ya saba baiwa matar El-Rufai damar shiga wajan a asirce ba saidai dubunsa ce ta cika.

Karanta Wannan  Bani ba ku, bazan koma jam'iyyarku ta ADC ba>>Gwamnan Zamfara ya gayawa Su Atiku

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *