
Dan takarar gwamnan jihar Gombe, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, Yayi Ritaya daga Limanci.
Malam ya bayyana hakane a wani Bidiyonsa dake ta yawo a kafafen sada zumunta inda yace, a kyaleshi yanzu ba zai zama Limamin kowane masallaci ba.
Malam ya kara da cewa, Watakila nan gaba ida ya tsufa ya koma jiran mutuwa zai ci gaba da limanci.
Saidai yace karantarwa ita ba zai daina ba.