
Da Duminsa: Najeriya ta zo ta daya cikin jerin kasashen da mutanenta suka fada gawurtaccen Talauci a Duniya cikin shekaru 3
Rahoton yace Mutane Miliyan goma sha bakwai da dubu dari tara ne,17.9M suka fada matsanancin Talauci a Najeriya
Hakan yasa Najeriya ta shiga kaban kasashe irin su Afghanistan dake da mutane Miliyan biyar da dubu dari ukku, 5.3M da suka fada Talauci.
Saurab kasashen da jama’ar su suka fada matsanancin Talauci a Duniya sune, Kyrgyzstan, Central Africa Republic, Da Guinea.
Majalisar Dinkin Duniya, United Nations Development Programme da the Oxford Poverty and Human Development Initiative ne suka fitar da wannan alkaluma a jiya Litinin.
Rahoton yace lamarin ya farune a tsakanin shekarun 2021 zuwa 2024.
Inda yace an samu koma baya idan aka kwatanta da shekarun 2018 zuwa 2021 da talauci ya ragu a Najeriya.
Rahoton yace wannan gwajin Talaucin da aka yi ba akan kudi bane kawai, an yi shine akan Samun ruwan sha, Ilimi, Kiwon Lafiya, wutar Lantarki, Tsafta, gidan zama da abinci me gina jiki.
Rahoton yace hakan na nufin an samu kaso 38.7 na karuwar Matalauta a Najeriya.
Rahoton yace jimullar wadanda ke cikin Talaucin ya karu daga mutane Miliyan 72.21 zuwa mutane Miliyan 90.07