Friday, October 16
Shadow

Yaje da niyyar sayen Mota ashe karya yake ya gudu da ita

Yaje wajan sayar da motoci yace zai sayi motar Toyota Tundra 2025 wadda kudinta Naira Miliyan dari da Talatin ne,130M

Yace a kawo masa makullin motar dan yaji kukan injin.

Daya daga cikin ma’aikatan kamfanin sayar da motar ya tafi ya dauko masa makullin motar.

Ya tayar kawai sai ya mamayeshi ya kulle kofar motar ya saka giya ya gudu.

Aka bishi da gudu, ya je ya buge kofar kamfanin sayar da motocin sannan ya hau titi ya buge wasu motocin

Daga karshe dai ya saka motar a ruwa.

Bayan an kamashi, shima ya ji ciwo a jikinsa, me kamfanin sayar da motar ya biya kudi aka kaishi Asibiti aka mai magani sannan aka mikashi hannun ‘yansanda.

Karanta Wannan  Idan na zama shugaban kasa, Yarbawa san fi baiwa mukami ba Hausawa ko Fulani ba>>Atiku Abubakar

Me kanfanin motar yace gyaran motar da sauran abubuwa zai kama Naira Miliyan 40 ne.

Saidai da ya je ofishin ‘yansanda dan jin ba’asin bincike, ya tarar an saki mutumin.

Me sayar da motar me suna Chima Edmund a hirar da yayi da jaridar Punchng yace an gaya masa cewa wai mutumin bashi da hankali ne.

Yace to amma shi yanzu ta yaya za’a barshi shi kadai zai yi asarar Naira Miliyan 40?

Danna nan dan kallon Bidiyon

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *