Matasa masu shirin fita Zàngà-zàngàr tsadar rayuwa sun gargadi hukumomi kan cewa kada a sake a harbi ko a kashe ko da mutum daya a cikinsu.
Sunce muddin aka yi hakan, to lallai zasu ajiye duk wasu bukatunsu su koma neman sai Bola Ahmad Tinubu ya sauka daga mulki.
Daya daga cikin wakilan kungiyar, Damilare Adenola ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar.
Ya kara da cewa ba zasu bari jinin ‘yan uwansu ya zuba a banza ba.