Wata babbar kotu dake babban birnin tarayya, Abuja ta haramta yin zanga-zanga.
Kotun tace ba’a amince wani dan zanga-zanga ya hau kan titin babban birnin tarayya Abuja ba da sunan zai yi Zàngà-zàngà.
Ministan Abuja, Nyesome Wike ne ya gabatar da wannan korafi a gaban kotun.
A baya dai masu zanga-zangar sun nemi a basu filin Eagle Square dan amfani dashi wajan gudanar da gangaminsu amma hukumomi suka kiya.
A yanzu masu zanga-zangar sun bayyana cewa ko an yadda ko ba’a yarda ba zasu yi amfani da filin.