Rahotanni daga jihar Borno na cewa, akalla mitane 19 ne suka mutu,wasu da dama suka jikkata bayan harin bam da dan kunar bakin wake yakai akan kauyen Kawuri dake karamar hukumar Konduga ta jihar.
Hakan na zuwane kasa da kwana daya bayan da bam ya tashi da wata mota ya kashe wani akawu dake aiki da karamar hukumar Damboa.
Hakanan a baya ma bamabamai na kunar bakin wake sun tashi a karamar hukumar Gwoza inda mutane akalla 30 suka mutu wasu 100 suka jikkata.
Jami’an tsaro sun fitar da sanarwar kiyaye kowane irin taron mutane a yanayin da ake ciki.