Monday, January 19
Shadow

Dan kunar bakin wake da ya tayar da Bàm ya kàshe mutane 19 a jihar Borno

Rahotanni daga jihar Borno na cewa, akalla mitane 19 ne suka mutu,wasu da dama suka jikkata bayan harin bam da dan kunar bakin wake yakai akan kauyen Kawuri dake karamar hukumar Konduga ta jihar.

Hakan na zuwane kasa da kwana daya bayan da bam ya tashi da wata mota ya kashe wani akawu dake aiki da karamar hukumar Damboa.

Hakanan a baya ma bamabamai na kunar bakin wake sun tashi a karamar hukumar Gwoza inda mutane akalla 30 suka mutu wasu 100 suka jikkata.

Jami’an tsaro sun fitar da sanarwar kiyaye kowane irin taron mutane a yanayin da ake ciki.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyo: Da in zabi shugaba Wanda ba musulmi ba ya min Adalci in samu Arziki gara in zabi musulmi yayi sanadin tafiyata kiyama>>Inji Wannan malamin mabiyin Shaikh Sani Yahya Jingir

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *