AMFANIN GOROBA GIDA 9 A JIKIN DAN ADAM
KADAN DAGA JIKIN AMFANIN TA
- Masu fama da cutar asma za su iya shan garin kwallon goruba a cikin tafashashen ruwa.
- Yana taimakawa masu samun matsala lokacin fitsari.
- Shan garinta a ruwan dumi na taimakawa masu karancin jini a ji.
- Goruba na maganin matsalar hawan jini.
- Haka zalika goruba na magance cutar basir.
- Yana kuma kare mutum daga kamuwa da cutar daji.
- Cin goruba na kara karfin namiji.
- Yana kuma rage kiba a jiki.
- Cin goruba na kara karfin kashi da hakora.
wallahu a’alamu.
“ FA’IDA GAME DA AMFANIN GORUBA AJIKIN ƊAN-ADAM „
GORUBA TANA MAGANI KAMAR HAKA:
1-Maganin basir
2-Maganin Hawan jini
3-Maganin ciwon qoda
4-Ciwon hanta
5-Ciwon shawara
6-Ciwon mara
7-Ciwon sanyi
8-Ciwon taipot (typhoid)
9-Ciwon maleriya(malaria)
10-Zafin jiki
11-quraje
12-Kashin jini
YADDA AKE AMFANI DASHI
za’a samu goruba dadama ayi garinsa ko asayo garinsa
1.mai fama da ciwon basir da typhoid zai zuba garinsa cokali 2 da garin arrabi cokali daya acikin madara yariqasha har sati daya.
2.Mai fama ciwon sanyi da ciwon mara ya samu garin goruba cokali daya da garin tafarnuwa cokali daya ya zuba a madara yasha sati biyu
3.Mai fama da ciwon malaria da zafin jiki ya samu goruba cokali biyu da garin rai dore cokali daya da garin zunzuna cokali daya ya hada ya zuba a madara yasha sati daya,
4.Mai fama da ciwon hawanjini da qoda yasami garin goruba cokali uku da garin ganyen dankali cokali biyu da garin zogala cokali biyu da garin ganyen tumatiri cokali biyu ya zuba a madara yasha sati uku
5.Mai fama da ciwon hanta ya samu garin goruba cokali biyu da garin kalkashi cokali biyu azuba aruwan zafi Asha har sati uku .
6.Mai fama ciwon quraje ya sami ya sami garin goruba cokali daya da garin goga masu cokali daya ya hada da madara yasha sati daya
7.Mai fama da ciwon shawara ya sami goruba cokali biyu da garin mujirya(jinjirya) cokali biyu da garin tafarnuwa cokali daya Asha da madara sati daya
8.Mai fama da kashin jini ya sami garin goruba cokali uku da garin sabara cokali daya da garin ganyen dorawa cokali daya Asha da madara sati daya
Abin lura, madaran shanu kuma kafi daya ne karya wuce, daga dandalin magungunan mata
A daure arika share (turawa/jama’a) domin Amafanuwan Al-umma Allah shi biya mana buƙatun mu albarkar Manzon SAW Ameen.
Shayin Goriba
Masu bibiyar AID Multimedia Hausa barkan mu da war haka muna muku fatan alkhairi gabaki daya.
Wannan dandanli namu mai albarka zai fara kawo muku abubuwan na suka shafir girke-girke domin karuwarku a yau da kullum a fannin girke-girke na gida namu da na kasashen ketare, kama daga abinci zuwa abin sha, na talaka da na masu hannu da shuni, shirin da ni Maman Hanan zan dinga shiryawa na kuma kawo maku, ina fatan zaku dinga jin dadin hakan.
Kamar dai yadda muka tsara a yau insha Allah za muyi somin tabi ne da shayin goruba (wato Doum palm tea) a turance.
Abubuwan da za’a bukata sun hadar da;
Gorubah
Lipton
kanunfari
Busheshshiyar citta ko danya
Cinnamon (girfa)idan ana bukata amma ba dole ba ne, sai kuma
Siga ko
Zuma.
Yadda za’a hada
Da farko zaku samu goruba, eh goruba dai tamu ta gargajiya( wanda aka cire ajikin daga kwallon) sai ki zuba a tukunya tareda kanunfari,citta),cinnamon(girfa), sai ki zuba ruwa dai dai bukata ki barshi ya tafasa bafa daga tafasa zaku sauke b, ki barshi ya tafasu sosai kafiin ki sauke ki tace ki zuba siga ko zum ki juya sossai
Amfanin shayin goriba a takaice;
Shi fa wannan shayin gorubar wani nau’ine na carbohydrate da fiber, yana magance matslar damuwa a ciki, cushewarsa da cunkushewarsa, yana rage kiba ko teba, yana kuma maganin kumburi, yana sauke ko maganin hawan jini.
Jama’a wannan shayin baya bukatar madara ko milo, shayi dai irin wanda kowa zai iya hadawa cikin sauki, wato ga saukin kashe kudi ga biyan bukata..
Shin kuma kuna son wannan shayin?
Wanne irin shayi ku ka fi so, me madara ko ruwan bunu?
Mu hadu a comment section domin jin raayoyinku.
Daga Shaheeda Ibrahim AKA Maman Hanan.