Mutumin mai suna Lawan Jikan Dada dan kasuwa ne da yake huldar kasuwanci da manyan bàŕayin daji masu ģàŕķùwa da mutane.
Duk abinda suka śàťò kamar shanu da sauran kaya shi yake zuwa ya saya a wajen su tare da ba su bayanan sirri, inda aka gano cewa aikin da yake yi kenan tsawon lokaci.