Mun samu labarin rasuwar yara biyu wadda iftila’in Gini ya faɗo musu a Anguwar Git Git dake Yarimaram ward Potiskum. Tare da raunata mutum ɗaya.
Tunidai shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Yobe, Dr. Mohammed Goje ya bada umarnin a yi gaggawa kai su Babban asibiti tare da biyan kuɗin magungunan da aka rubuta musu.
Yanzu haka Uwar tana kwance a Babban Asibitin Kwararru dake garin Potiskum domin cigaba da jinya. Inda aka garzaya da yaran biyu zuwa gida domin yi musu jana’iza.
Muna roƙon Allah ya karɓi shahadarsu baki ɗaya.
Mahaifiyar tasu kuma Allah ya bata lafiya tare da haƙurin jure wannan Babban rashi.
JAN HANKALI
Wanann shekarar mun samu al’umma da dama wadda gine gine ya faɗo akansu tare da asarar rayuka da dama.
Dan Allah duk wadda gininsa ya nuna alama yayi haƙuri ya fita. Domin rayuwarka da iyalanka ta fi komai.
Har yanzu dai kar a manta idan wani al’amari ya faru da ya shafi taimakon gaggawa za a iya tuntuɓar ɗaya daga cikinmu.
Ahmed Haruna Daya
Abdul Atiyaye
Ali Shitu Potiskum
Yusuf Maina
Mohammed Kawuwale