Jarumar mai suna Sadiya Abdulƙadir wacce aka fi sani da (Sareena) sabuwar Jaruma ce duk da cewa ta ɗan kwana biyu a masana’antar ta Kannywood ana damawa da ita a fagen shirya fina-finan Hausa wadda ƴar asalin Jihar Bauchi ce ƙaramar hukumar Azare.
Fim na farko da ta fara yi tun bayan shigowarta masana’antar fim ne mai dogon zango mai suna (Aliya) wanda ake haska shi a (Youtube Channel) na Ali Jita, wato (Ali Jita Multimedia).
Yanzu haka dai Jarumar ta faso gada-gadan da zafinta domin cigaba da aikinta na faɗakarwa cikin fina-finan Hausa domin inganta tarbiyyar al’umma.
Photo Credit: Dk Photography
Wane fata zaku yi mata ?