Thursday, October 3
Shadow

Sojoji Śun Ķashe ‘Ýan Ța’àďda 1,166, Yayin Da Suka Kama 1,096, Inji Hedikwatar Tsaro

Daga Bello Abubakar Babaji

Hedkwatar tsaro (DHQ) tace jami’anta sun kashe ƴan ta’adda guda 1,166 tare da tsare wasu 1,096 acikin kwana 29 a faɗin Nijeriya.

Daraktan watsa labarai na ofishin, Manjo-Janar Edward Buba ya faɗi hakan a Abuja, a lokacin da ya ke ganawa da manema labarai kan ayyukan jami’an tsaro, a ranar Alhamis.

Ya ce, jami’an sun yi nasarar ceto mutane 721 da aka yi garkuwa da su.

Sannan, sun kuma ƙwato makamai 391 da wasu nau’ukan bindigu da kayan yaƙi da adadinsu ya kai 15,234 acikin wata guda.

Ya ƙara da cewa, sun yi nasarar kamo manyan ƴan ta’addan da kwamandodinsu a yayin gudanar da ayyukansu cikin watan.

Karanta Wannan  Gwamnatin Tinubu ta bada umarnin a fara sayar da man fetur akan sama da Naira Dubu daya kowace lita

Waɗanda aka kama a yankin Arewa-maso-Gabas sun haɗa da; Munir Arika, Sani Dilla (aka Ɗan Hausawan Jibilarram), Ameer Modu, Ɗan Fulani Fari Fari, Bakoura Araina Chikin, Dungusu, Abu Darda da Abu Rijab.

A yankin Arewa-maso-Yamma kuma waɗanda suka shiga hannu sun haɗa da; Kachalla Ɗan Ali Garin Fadama, Kachalla Dan Mani Na Inna, Kachalla Basiru Zakariyya, Sani Bakatsine, Inusa Zangon Kuzi, Ibrahim, Tukur and Kamilu Buzaru da sauran su.

Hakan kuma ya ce, kimanin mayaƙan Boko Haram/ISWAP 2,742 tare da iyalansu ne suka miƙa wuya wa jami’an tsaro da kuma ƙwato wasu muggan makamai daga gare su.

Kazalika, Buba ya yi ƙarin haske game da kula da binciken su ke yi kan waɗanda aka kama da laifin satar ɗanyen mai, ya na mai cewa su na cigaba da sanya ido a lamarin da ma sauran laifukan ta’addanci da suka addabi baki ɗaya sassan Nijeriya.

Karanta Wannan  Masana'antar Kannywood Ta Samu Ƙaruwar Galleliyar Sabuwar Jaruma Daga Jihar Bauchi

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *