Akwai yiyuwar Shugaban kasa,Bola Ahmad Tinubu zai canja wasu ministoci a majalisarsa ta zartaswa.
Hakan wani mataki ne na cire ministocin da basa tabuka wani abin azo a gani.
Shugaban dai ya jima yana fuskantar matsi akan ya canja ministocin da basa yin aikinsu yanda ya kamata.
A shekarar da ta gabata ne dai shugaban kasar ya kafa wani tsari na auna kokarin ministocin inda yayi gargadin duk wanda ba ya kokari za’a koreshi daga aiki.