Kamfanin mai na kasa,NNPCL ya koka da cewa bashin masu kawo man fetur ya mai yawa.
Kamfanin ya tabbatar da hakan ne ta bakin me magana da yawunsa, Olufemi Soneye inda yace kamfanin na fama da matsalar bashin masu kawo mai.
Yace hakan na barazana ga wadata kasarnan da man fetur.
Saidai ya bayyana cewa, NNPC ba zata yi kasa a gwiwa ba wajan ganin ta ci gaba da gudanar da aiki a matsayin babbar me wadata kasarnan da Man fetur.