Wani sabon rahoton da ya bayyana na nuni da cewa za’a kara farashin man fetur zuwa akalla Naira 1000 akan kowace lita.
‘Yan kasuwar man fetur din ne suka bayyanawa jaridar Vanguard hakan a wata zantawa da ta yi dasu.
Hakan na zuwane bayan da kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya koka da bashin da ya masa yawa na ‘yan kasuwar man fetur da suke kawo man a matsayin bashi.
‘Yan kasuwar dai da yawa wanda na kssa da kasa ne aun ce sun daina kawowa Najeriya mai a bashi har sai an biyasu bashin da suke bi.
Hakan yasa gwamnati zata iya kara farashin man fetur din dan ta samu kudaden da zata biya wancan bashin da ake binta.
Ko kuma ta raba ta biya rabi ‘yan kasa su biya rabi, hakanan kuma hakan na nufin lallai fa sai an kara farashin man saboda a yanzu gwamnati bata da kudin da zata ci gaba da biyan tallafin da take biya,hakalinta ya koma kan maganar biyan bashi.
A baya dai hutudole ya kawo muku yanda kamfanin man na kasa,NNPCL ya bayyana cewa tabbas ana binsu bashin bayan da a baya sukaita karyata hakan.
A kididdigar da jaridar ta vanguard ta yi,tace wasu daga cikin ‘yan kasuwar sun bayyana mata cewa farashin sayen man fetur din a Depot zai kama naira 1200 ne akan kowace lita,a wannan farashin ba’a saka kudin dakon man zuwa gidajen man fetur din ba.
Dan hakane Jaridar tace idan aka saka kudin dakon man fetur din da sauran kudaden da za’a kashewa man kamin ya kai ga gidan man da za’a fara sayarwa da mutane masu ababen hawa, farashin lita zai kama akan naira 1,405 akan kowace lita.