Tsohon sanata da ya wakilci mazabar Adamawa ta Arewa a majalisar tarayya,Sanata Elisha Abbo ya sake bayyana a wata badakala wadda ke da kamanceceniya da irin badakalolin da ya shiga a baya.
Sanata Abbo a wannan karin Bidiyon sa ne ya bayyana yana lalata da wata matar aure me suna Mrs. Wange Minso Kwagga.
Bidiyon dai ya watsu sosai a kafafen sada zumunta abba saboda tsiraici dake cikinsa ba zamu iya nuna muku shi a shafinmu ba.
A bangaren matar, Mrs. Kwagga ta fito ta bayyana nadama akan abinda suka aikata ita da sanatan inda tace yayi amfani da halin matsin da take ciki ne ya cimma burinsa akanta.
Sanata Elisha Abbo wanda yaci zabe a shekarar 2023 saidai daga baya kotu ta soke zaben nasa a watan October na shekarar.
A baya dai sanata Abbo ya shiga wata tirka-tirka inda aka jishi ya je sayen mazakutar roba da wasu da ake zargin matan banza ne ko ‘yan matansa a Abuja.
Matar dai tace bata sani ba sanatan ya dauki hoton bidiyonta yayin da suke lalata.
Tace kuma zata kaishi kotu nan gaba kadan dan kwatar hakkinta.
An dai yi kokarin jinnta bakin sanatan amma ya kulle duka wayoyinsa ko an kira basa shiga.