Wani dalibi a makarantar Apalachee High School dake Winder a jihar Georgia ta kasar Amurka me kimanin shekaru 14 ya bude wuta akan dalibai da malamai a makarantar.
Hakan yayi dalilin mutuwar mutane 4 wanda 2 daga ciki malamai ne sai kuma biyu dalibai sannan wasu 30 sun jikkata dalilin lamarin.
Hukumomi sun bayyana cewa an kama dalibin
Hakanan duka makarantun dake gundunar an kullesu na dan lokaci saboda tsaro kuma an baza jami’an tsaro sosai.
Saidai Har yanzu ba’a sake gano wani lamarin ba inda ake tsammanin dalibin shi kadai ya aikata wannan aika-aika.