Dan jarida daga kasar Ghana, AbdulHakim Auwal ya kafa tarihin zama wanda yafi dadewa yana rungume da bishiya.
Dan shekaru 23 ya shafe awanni 24 da mintuna 21 yana rungume da bishiyar.
Hakan yasa ya shiga kundin tarihin Duniya na Guinness World Record.
Wanda ke rike da wannan matsayi a baya ‘yar kasar Uganda ce me suna Faith Patricia Ariokot wadda ta yi awanni 16 tana rungume da bishiyar.