Friday, December 5
Shadow

Mahajjaci dan Najeriya ya rasu a kasar Saudiyya

Rahotanni sun bayyana cewa, mahajjaci dan Najeriya daga jihar Legas ya rasu a kasar Saudiyya.

Idris Oloshogbo dan shekaru 68 ya rasu ne bayan ya kammala dawafi yana cikin cin abinci.

Jami’an lafiya na kasar Saudiyya sun tabbatar da rasuwar Idris.

Sakataren hukumar kula da walwalar Alhazai ta jihar Legas, Saheed Onipede ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace suna mika ta’aziyya ga iyalan mamacin.

Karanta Wannan  Subhanallahi: Ji yanda Mahajjaciya 'yar Najeriya ta kash-she kanta a kasar Saudiyya ta hanyar fadowa daga sama

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *