Man kadanya na da amfani sosai a jikin dan adam kuma maza da mata na iya amfani dashi.
Wani shahararren likita a kasar Amurka me suna Dr. Debra Jaliman ya bayyana cewa za’a iya shafa man kadanya a kusan dukkan jiki hadda a saman al’aura ta maza da mata.
Idan azzakarinka na kaikayi, zaka iya shafa man kadanya dan ya daina.
Hakanan idan Azzakarinka na kumbura shima zaka iya shafa man kadanya dan ya daina.
Idan Azzakarinka na bushewa sosai musamman lokacin sanyi, shima zaka iya shafa man kadanya.
Saidai masana sun yi gargadin kada a saka man kadanya a cikin azzakari ko a shafashi a yi jima’i dashi.