Sunday, May 18
Shadow

Nine zan lashe zaben shugaban kasa na 2027 saboda PDP ta mutu murus>>Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa a jami’iyyar NNPP, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa,shine zai lashe zaben shekarar 2027 saboda PDP ta mutu.

Ya bayyana hakane a Katsina bayan kaddamar da ofishin jam’iyyar a kan hanyar IBB Way.

Kwankwaso yayi kira ga mutanen jam’iyyarsa da kada su yadda a yaudaresu da Taliya da kudi yayin zabe inda ya jawo hankalinsu kan su ci gaba da aiki tukuru dan ci gaban jam’iyyar.

Karanta Wannan  Mun daina fargabar da muke yi akan Muslim-Muslim saboda Gwamnatin Tinubu ta mana Adalci>>Inji Kungiyar Kiristanci ta CAN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *