Ba Gaskiya Ba Ne Maganar Da Sheíkh Sani Yahaya Jingir Yayi, Saboda Bamu Wallafa Labarin Dake Cewa Tinubu Bai San An Ƙara Farashin Man Fetur Ba, Idan Kuwa Mun Wallafa Ya Bamu Hujja, Martanin Jaridar Daily Trust Ga Shiekh Jingir.
A baya dai malam ya bayyana cewa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima basu sani ba aka kara kudin man fetur.
Inda malamin yayi ikirarin cewa, jaridarta Daily Trust ce ta ruwaito hakan.
Lamarin ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sadarwa.
Inda da yawa suke ganin cewa bai kamata malamin yayi wannan magana ba.
Me zaku ce ?