Rahotanni sun bayyana cewa farashin man fetur daga matatar man Dangote zai iya kaiwa Naira 857 zuwa 865.
Kamfanin man fetur na kasa, NNPCL ya bayyana cewa, zai dauki man daga matatar man Dangote a farashin Naira 960 zuwa 980 akan kowace lita inda zai sayarwa da ‘yan kasuwa akan farashin 850 zuwa 840.
Saidai babu tabbacin ko za’a samu farashin bai daya a duka gidajen man sayar da fetur din a Najeriya.
Me kula da yada labarai na kamfanin na NNPCL Olufemi Soneye ya tabbatar da cewa a ranar 15 ga watan Satumba ne zasu fara dakon man fetur din daga matatar man Dangote.