Tsohon shugaban kasa,Abdulsalam Abubakar ya gayawa Gwamnati cewa wahalar da ake ciki a kasarnan ta yi yawa.
Ya bayyanawa manema labarai cewa,mutane da yawa a yanzu basu da kudi inda kudin mota da sauran ababen hawa suka karu ga kudin makarantar yara ya karu kuma mutane basa iya cin abinci sau 3 a rana.
Yace shi da wasu masu fada a ji sun baiwa gwamnatin tarayya shawarar yanda za’a fita daga cikin halin da ake ciki.
Daya daga cikin hanyoyin kamar yanda yace sune gwamnatin ta sayi abinci ta rika sayarwa a farashi me sauki.
Ya kuma bayar da shawara ga masu shirin yin zanga-zangar tsadar rayuwa ta ranar 1 ga wata October da kada a tayar da hankali a yi ta cikin lumana.