Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya tabbatar wa ‘yan ƙasar cewa gwamnatinsa za ta mayar da hankali wajen kawo muhimmin sauyi a harkar ci gaban ƙasar, da samar da abinci da makamashi da tsaro da ilimi da kuma tsarin tattalin arziki mai ɗorewa.
Yayin da yake ganawa da ƙungiyar tsoffin jagororin majalisar dokokin ƙasar, ƙarƙashin jagporacin tsohon shugaban majalisar dattawan ƙasar, Sanata Ken Nnamani, shugaba Tinubu ya ce bai zama shugaban Najeriya domin cin wata riba ta ƙashin kai ba, face don bauta wa ƙasar.
”Ban zama shugaban Najeriya, don samun kuɗi ko cin wata riba ba, na zo ne don yi wa ƙasa aiki, kan haka ne nemi ƙuri’un ‘yan Najeriya kuma suka ba ni”, in ji shugaban ƙasar, kamar yadda Bayo Onanuga mataimakinsa na musamman kan kafofin yaɗa labarai, ya bayyana cikin wata sanarwa.
Sanarwar ta ce manyan tsoffin jagororin majalisar dokokin ƙasar 16 ne suka halarci zaman, ciki har da tsoffin shugabannin majalisar dattawa na da wakilai da mataimakansu.
Shugaba Tinubu ya kuma yaba wa tsoffin shugabannin majalisar dokokin ƙasar bisa ziyarar da suka kai masa, wadda ya ce za ta ƙarfafa masa gwiwa kan ƙudurin gudanar da gwamnatinsa.