Wednesday, December 11
Shadow

Yadda ake gane mace mai ni’ima tun kafin aure

Mafi yawancin lafiyayyun mata na da ni’ima inda wasu kuma rashin lafiya ko rashin wadata da kwanciyar hankali da samun cima me kyau ke hanasu samun ni’ima.

Ni’ima a wajan mace ta hada abubuwa da yawa, ba kawai tana nufin dadin farjin mace bane ko kuma ruwan dake gabanta ba.

Tabbas Ruwan dake gaban mace shine jagora a wajan ni’imarta amma ba shi kadai bane.

Ni’ima a tattare da mace ta hada da:

Surar jikinta.

Laushin fata.

Nonuwa masu daukar hankali.

Mazaunai masu daukar hankali.

Murya.

Da kuma iya soyayya.

Ruwan gaba.

Iya Kwanciyar aure.

Gashi.

Kwalliya.

Macen data hada wadannan abubuwa tabbas tana da ni’ima kuma mijinta zai ji dadin tarayya da ita sosai.

Surar jiki halittace daga Allah, wadda wata zaka ganta tsayuwarta kawai ko tafiyarta na da daukar hankali, wata kuma zaka ga kamar Namiji, sam surar jikinta kamar ba ta mace ba.

Karanta Wannan  HOTUNAN BIKI: Hajiya Dakta Maryam Shetti ta yi aure

Wani yafi son me jiki wani madaidaiciya wani siririya, dan haka sura takan zo daidai dan son zuciyar namiji.

Laushin Fata yakan samu ne idan akwai kula musamman idan mace a gidan wadata ta fito, ba man shafawa ne kadai ke sa laushin fata ba, hadda cima.

Idan mace na samun abinci me gina jiki zaka ga ko da bata shafa mai me tsada can sosai, fatarta na sheki kuma tana da laushi.

Nonuwa suma halittace wadda wata zaka ga nata manya ne wata kuma kanana ne, macen da kirjinta ya ciko, ta fi daukar hankali kuma zata fi yiwa namiji dadi wajan kwanciyar aure, duk da yake maza kan so girman nono daban-daban.

Karanta Wannan  Hotuna:Wannan budurwar na neman mijin aure

Mazaunai na taka rawa sosai wajan cikar ni’imar mace, mace me madaidaitan mazaunai wanda suka dan tashi sama ko kuma suka fito waje tafi dadin sha’ani wajan kwanciyar aure kuma ni’imarta ba data take da wadda ke da shafaffun mazaunai ba.

Murya na da matukar tasiri wajan cikar ni’imar mace, macen dake da murya me dadi, muryar kawai na iya tayar da hanlalin namiji yaji yana sha’awarta, ballantana ma idan an zo kwanciyar aure, shagwaba da kukan dadin da zata rika yi da muryar tata zasu yi tasiri sosai wajan gamsar da namiji.

Iya soyayya ni’imace babba dake tattare da macen da ta iya, kulawa da namiji, kalamai masu dadi,kula da kanta, kallo, iya taso da sha’awar namiji, girki me dadi, dadai sauransu.

Ruwan gaba ginshiki ne wajan cikar ni’imar mace, shima cima tana taimakawa sosai wajan samunsa,macen dake samun abinci me gina jiki da kuma kwanciyar hankali zata samu ruwan gaba sosai, macen dake cikin wahala da kuma rashin cin abinci me gina jiki ba lallai ta samu ruwan gaba yadda ake so ba.

Karanta Wannan  Alamomin namiji mai karfin sha'awa

Ko da mace bata da ruwan gaba akwai hanyoyi da yawa ciki hadda mai da ake amfani dashi dan tabbatar da gabanta yayiwa me gida dadi.

Iya Kwanciyar aure idan dai mace ba bazawara bace, mijine ya kamata ya koyawa matarsa yanda yake so.

Gashi ma ni’imane a wajan mace, musamman idan mace ta iya kula dashi yana sheki yana kanshi to tabbaa shima cikar ni’imane.

Kwalliya a gurin mace ni’imace kuma dole kowace mace ta dage taga tana kwalliya iya daidai gwargwado.

1 Comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *