JARABTA: Cikin Kwanaki Uku A Jere, Ya Rasa Matarsa Da Yaransa Biyu.
Wannan bawan Allah mai suna Adamu Manzo ya gamu da jarabawar rashi.
Shekaran jiya Lahadi babban d’ansa ya rasu aka yi masa jana’iza jiya Litinin, bayan an dawo daga makabarta jaririn da aka haifa masa da kwana d’aya ya rasu shi ma aka yi jana’izar sa, inda a jiya Litinin din, Allah mai yin yadda Ya so sai kuma ga shi an wayi gari da rasuwar matar sa wacce ita ce mahaifiyar yaran guda biyun da suka rasu.
Tuni aka yi mata sallar jana’iza a safiyar yau Talata a unguwar Dawaki Kofar Sarkin Doya, dake jihar Gombe.
Hakika wannan jarrabawa ta girmama matuka. Allah Ya gafarta musu.