INNALILLAHI WAINNA ILAIHI RAJIUN:
Ana Juyayin Mutuwar Magidanci Da Daukacin Iyalansa Da Ya Goyo A Bisa Babur.
Da safen yau Lahadi wani magidanci ɗauke da matarsa da ‘ya’yansa akan mashin su 6 sun haɗu da ajalinsu sakamakon hatsari inda babbar mota kirar DAF tabi takansu a bakin gidan ruwa (Zamfara State Water Board) kusa da Gusau Hotel.
Hatsarin ya jefa al’ummar yankin cikin alhini da jimami.
Allah ya jiƙansu da rahama ya gafarta musu.