Atiku ya bukaci majalisa ta ƙara wa’adin mulkin Shugaban ƙasa zuwa shekara 6 sannan a mayar da mulkin Najeriya karba-karba tsakanin Kudu da Arewa
Madugun yan adawa a Najeriya Atiku Abubakar, ya rubutawa majalisar dokokin ƙasar nan yana bayar da shawarar a yi wa kundin tsarin mulki kwaskwarima domin mayar da wa’adin mulki zuwa shekara shida ga Shugaban kasa da Gwamnonin jihohi.
Takardar da ya aike wa kwamitin majalisar dattawa mai kula da tsarin mulki, Atiku ya kuma bayar da shawarar a mayar da mulkin Najeriya ya koma tsarin karba-karba a matakin Shugaban kasa tsakanin yankunan Arewa da Kudu.
Menene ra’ayinku?