Tsohon hadimin shugaban kasa,Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa, Peter Obi yafi Dr. Rabiu Musa Kwankwaso a siyasance.
Muhawara dai ta kaure a kafafen sada zumunta bayan da Kwankwaso yace yafi Peter Obi tasiri a siyasa inda yace amma duk da haka zai iya zama mataimakinsa.
Saidai wannan jawabi nashi ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa hakane wasu ke cewa basu yadda da maganar tashi ba.
Tsohon hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad ya bayyana cewa Yana girmama Kwankwaso amma maganar gaskiya a siyasance musamman lura da sakamakon zaben shekarar 2023, Peter Obi yafi Kwankwaso.
Kwankwaso dai ya samu kuri’u 1,496,687 wanda kuma a jihar Kanone kawai ya shiga gaba amma Peter Obi ya samu kuri’u 6,101,533 inda kuma ya shiga gaba a jihohi 11.