‘Yansanda a jihar Legas sun kama wata budurwa me suna Victoria Effiong, inda aka kaita kotu bisa zargin ta cinyewa saurayinta kudi da sauran kaya amma taki yadda ta aureshi.
Jimullar kudaden d Victoria ta karba a hannun saurayin nata sun kai Naira miliyan 2.8.
Jami’in dansanda dake gabatar da kara a kotun magistre dake Legas, Inspector Chinedu Njoku ya bayyana cewa, budurwar ta kuma samu wayar iphone da kudinta ya kai Naira 240,000 daga wajan saurayin.
Sannan ya sai mata agogo da kayan sawa da jaka da takalma da suka kai na Naira 350,000.
Sannan ya bata jimullar kudin abinci na naira 868,000.
Akwai kuma wata Naira 300,000 data taba cirewa daga asusun ajiyarsa na banki.
Lamura sun rinchabene bayan da saurayin nata me suna Dominic Asuquo ya gano tana shirin auren wani can daban bashi ba duk da yake cewa ta gabatar dashi din a wajan iyayenta.
Saidai Victoria ta karyata cewa suna soyayya da Dominic inda tace tabbas ya bata wayar iphone da wata waya da kuma kudade amma yasan tana soyayya da wani kuma ta sha gaya masa ya daina bata abubuwa.
A karshe dai Alkalin kotun ya bayar da belinta akan Naira 200,000 da kuma mutane 2 da zasu tsaya mata.
An dage sauraren karar sai zuwa ranar 28 ga watan Nuwamba.