Monday, December 16
Shadow

DA ƊUMI-ƊUMI: Matatar Mai Ta Ɗangote Za Ta Fara Sayar Da Mai Kaitsaye Ga Ƴan Kasuwa

Bayan cikar wa’adin yarjejeniyar da suka ƙulla da kamfanin mai na ƙasa NNPC tun da farko, yanzu haka matatar mai ta Ɗangote za ta fara saida mai kaitsaye ga duk wasu ƴan kasuwa masu buƙata.

A Rahoton da Jaridar Dokin Ƙarfe TV ta samu, hakan na zaman wani mataki ne na buɗe ƙofa ga kowa da kowa da ke buƙatar sayen man ba wai iya NNPC kawai ba. Kowane ɗan kasuwa da ke buƙatar mai daga yanzu zai iya zuwa matatar man ta Ɗangote kaitsaye su yi ciniki a tsakaninsu.

Wannan tsari, zai kuma ba wa kasuwa dama ta yi halinta da kanta batare da an ƙayyade farashi ba, inda matatar za ta saida man kaitsaye ga ƴan kasuwa a farashin da ta ke so ko mai saya yake so.

Karanta Wannan  Ji yanda ake ciki kan maganar mafi karancin Albashi tsakanin Gwamnati da NLC, inda ake tunanin za'a sake komawa yajin aiki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *