Jam’iyyar Labour party ta yi maraba da maganar da tsohon gwamnan Kano Dr. Rabiu Musa Kwankwaso yayi na cewa zai iya zama mataimakin Obi a zaben 2027.
A wata hira ce dai da aka yi Kwankwaso ya bayyana haka inda yace idan an bi tsari me kyau aka cimma yarjejeniya duk da yana sama da Peter Obi a siyasa da shekaru zai iya zama mataimakinsa.
Sakataren jam’iyyar Labour Party, Umar Farouk ne ya bayyana haka inda yace amma kada Kwankwaso ya bata rawarsa da tsalle saboda kalaman cewa yafi Peter Obi shahara a siyasa.
A baya dai Peter Obi da Kwankwaso sun so hadewa amma lamarin bai yiyu ba, saidai a wannan karin ko lamarin zai tabbata?