Taliya na da saukin Dafawa kuma ana hadata da abubuwa daban-daban wajan ci, irin su wake, shinkafa, Makaroni da sauransu.
Idan Taliya za’a dafa wadda babu komai a cikinta watau fara ba dafa duka ba.
Kawai ruwa za’a saka babban Kofi uku a tukunya a barshi ya tafasa, sai a saka taliya leda daya a ciki.
A barta ta dahu amma kada ta wuce minti 10 zuwa 15 sai a sauke, idan akwai sauran ruwa a tace idan kuma babu sai aci da abinda ake so watau Miya ko wani abu daban.