Sunday, January 5
Shadow

Kasar Namibia ta nemi Najeriya ta taimaka mata yin yaki da cin hanci

A kokarinta na yaki da rashawa da cin Hanci, Kasar Namibia ta nemi taimakon Najeriya wajan yaki da cin hanci inda tace tana neman shawarar Najeriyar ne saboda yanda kasar ke da kwarewa a fannin.

Kasar ta Namibia ta samu ci gaba sosai saidai tana fama da matsalar rashawa da cin hanci wanda hakan yasa mutane basu da yadda da gwamnatin tasu.

Kallon Nasarar da hukumomin yaki da rashawa da cin hanci na EFCC da ICPC ke samu yasa kasar ta Namibia ta nemi taimakon Najeriya wajan yaki da rashawa a kasarta.

Kasar tana neman Najeriya ta taimaka mata wajan kafa nata hukukomin na yaki da rashawa da cin hanci.

Karanta Wannan  Gwamnati ce zata kayyade farashin man fetur dina>>Inji Dangote

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *