Friday, January 23
Shadow

Duk da akwai wahala amma sai Gwamnati ta ci gaba da tsarin da take kai a yanzu na tsawon shekaru 15 kamin Najeriya ta ci gaba>>Bankin Duniya

Bankin Duniya ya baiwa Gwamnatin Najeriya shawarar cewa ta ci gaba da tsarin da take kai a yanzu na tsawon shekaru 10 ko 15 idan tana son samun ci gaba ba a Afrika kadai ba harma da Duniya baki daya.

Wakilin bankin Duniyar, Indermit Gill ne ya bayyana haka a wajan wani taron tattalin arziki da ya gudana a Abuja.

Ya kawo tsare-tsaren gwamnati na cire tallafin dala da mai da saransu wanda ya ce ya kamata a ci gaba da aikatasu dan samun ci gaba me dorewa.

Saidai a yayin da yake jawabin, an rika masa ehon ba’a son wannan shawara tasu ta bankin Duniya amma du da haka yace ba lallai ne a yadda da abinda yake fada ba amma gaskiyace.

Karanta Wannan  Biyo bayan nuna goyon baya ga Trump da goyon bayan Shi ya kawo Khàrì Najeriya, Fitsararriyar mawakiyar Amurka, Nicki Minaj ta rasa mabiya Miliyan 4 a shafinta na sada zumunta

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *