A yayin da majalisar Dattijai ke tattauna batun kirkirar kudirin dokar da zai samar da ma’aikatar wayar da kai akan ta’ammuli da miyagun kwayoyi da dawo da wanda suke cikin harkar kan tafarkin daidai, Sanata Kawu Sumaila ya zargi Sanatoci da hannu a harkar.
Sanata Sumaila ya bayyana cewa, akwai sanatoci da yawa dake da alaka da masu safarar kwaya da kuma wanda ma suna shanta.
Yace akwai wanda suke da tulin miyagun kwayoyin a gidajensu da mazabunsu, sannan akwai da yawa wadanda suke amfani da miyagun kwayoyin lokacin zabe su baiwa matasa dan cimma burikansu na siyasa.
Yace dan haka ta kansu ya kamata a fara wannan gyara.
Yace idan sun yi gaddama dukansu su je a musu gwayin shan miyagun kwayoyi sannan kuma kowa ya rantse da Qur’ani da Baibul cewa baya harkar.
Sanata Sumaila ya kara da cewa ya kamata duk wani dan siyasa da yake neman tsayawa takara a masa gwajin shan kwaya kamin a barshi ya tsaya takarar.
Yace ta hakane za’a kawo gyara.
Saidai mataimakin kakakin majalisar, Barau Jibrin ya bayyana cewa, maganar ta sanata Kawu Sumaila bata da alaka da tattaunawar da ake dan haka ba za’a dauketa ba.